News
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta kama wata matar aure bisa zargin kashe ’yar kishiyarta mai shekaru uku ta hanyar shaƙe ta har lahira a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta jihar.
Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce ana zargin matar ta aikata kisan ne sakamakon zafin kishi, bayan da ta yi zargin cewa mijinta ya yi watsi da ita da ’ya’yansu uku, tare da fifita amaryarsa.
Nada Mataimaka Na Musamman (SAs) Guda 4,000 Nayi Ba Matsala Ba Ce —Gwamnan jihar Edo
Ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Yuli, lokacin da mahaifiyar yarinyar ta bar ta a hannun wani ɗan uwa domin zuwa Kasuwar Tsakiyar Kaiama. A cewar ’yan sandan, wadda ake zargin ta yaudari yarinyar tare da fitar da ita daga gida zuwa wata gona da ke kusa, inda ake zargin ta shaƙe ta
SP Ejire-Adeyemi ta ce binciken da jami’an ’yan sanda suka fara gudanarwa nan take ya kai ga kama wadda ake zargin. Ta ƙara da cewa yayin da ake yi mata tambayoyi, matar ta amsa laifin, tana mai cewa fushi da kishi ne suka sa ta aikata hakan sakamakon wata doguwar takaddama ta cikin gida.
Kakakin ta ce an kammala binciken farko kan lamarin, kuma an gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsantsan, tare da sanar da jami’an tsaro duk wani bayani da zai taimaka wajen dakile aikata laifuka da kama masu hannu a cikinsu.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News5 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News16 hours ago
A Kasa Mai Mabiya Addinai Daban-daban, Bai Kamata A Sanya Addini Cikin Rudanin Siyasar Da Ke Cike Da Takaddama Ba. —Sheikh Gumi
