Connect with us

News

Auren Zawarawa Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne — Sheik Hadi MaiHula

Published

on

IMG 20260812 WA0000

Daya daga cikin fitattun Malaman Addinin Musulunci a nan Kano Sheik Alaramma Hadi Inuwa Maihula Sanka ya ce Auren zawarawa da gwamnatin Jihar Kano ta yi Haramun ne domin Allah madaukakin Sarki bai dorawa bawansa dole yayi Aure ba, sai wanda yake da iko.

Sheik Hadi MaiHula ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da ‘yan Jaridu a nan Kano da yammacin talatar nan.

An Cafke Mutane Biyar Kan Safarar Miyagun Ƙwayoyi Zuwa Gidan Yari Ta Jiragen Sama Marasa Matuka

Ya ce al’qur’ani mai girma yayi bayanin cewa fitar da Zakka da zuwa aikin Hajji da kuma yin Aure sai wanda yake da ikon yi, yana mai cewa Aure Addini ne, Amma diban kudin talakawa da gwamnatocin jihohi ke yi domin yin Auren zawarawa ko Auren gata “Haramun ne.” Ana kashe kudaden al’umma a hanyoyin da basu da ce ba, yayin da mutanen Kano suka rasa ingantaccen Ruwan Sha da wadatattun asibitoci.

“Da Aure, Zakka da zuwa aikin Hajji ba’a taba dorawa wani ya zama Dole ba matukar bashi da ikon,” inji Malamin.

“Allah yayi bayani a cikin Suratul Nur da Hadisan da Imam Muslim da Bukhari suka rawaito,” inji MaiHula.

Advertisement

Malamin ya ce wasu daga cikin shugabannin da suka yi a baya ma sunyi nadamar aikata hakan, yana mai Jan hankalin gwamnatin Jihar Kano ta da dakatar da aikata hakan a nan gaba.

“Garin Kano da babu wadatattun asibitoci, babu wadatattun kwararrun likitoci, babu Ruwan Sha, Mutanen da suka yiwa al’umma aiki wato ‘Yan Fasho ba’a gama biyansu ba, amma za’a kwashi makudan kudaden ayi abun da bai da ce ba,” inji MaiHula.

“Tun daga Gwarzo ko Takai ko Tsanyawa al’umma suke tahowa asibitin kwararrun na Murtala, kuma asibitin nan tun 1928 aka yi shi, me yasa baza a gina irin asibitin a Takai ko Tsanyawa ko Gwarzo ba ?” Inji Alaramma.

Daga nan yayi fatan gwamnatin Jihar Kano da sauran jihohi da suke da tunanin Ire-iren wannan Aure zasu dena, yana mai cewa Idan akayi Auren, gwamnatin zata ciyar musu da Matar ne ko kuma zata dauki Nauyin biyar kudin Hakika idan Matan sun Haihu, inda ya kara da cewa maimakon haka kamata yayi gwamnatin Jihar Kano ta koya musu sana’o’in dogaro da kai maimakon Barnatar da dukiyara Al’umma a hanyar da bata da ce ba da sunan Auren Gata.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending