Connect with us

News

Gobara Ta Tashi A Bankin Access Da Wani Gida A Kano

Published

on

Kano Fire Service (1)

Gobara ta tashi a wasu wurare biyu daban-daban a Jihar Kano, ciki har da reshen Bankin Access da ke Dawanau, a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, da kuma wani gida a Sabuwar Gandu, Sheka Gari, Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya fitar.

KANO: Mutum 4 Daga Cikin Mutane 16 Da Wani Gini Ya Rufta A Kansu A Dala Sun Rasa Ransu

Sanarwar ta ce gobarar farko ta tashi ne da misalin ƙarfe 1:17 na rana ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2026, a reshen Bankin Access da ke Dawanau, bayan hukumar ta samu kiran neman agaji daga wani mutum mai suna Michael.

Jami’an kashe gobara na tashar Dawanau sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka tarar da gobarar ta kama janareta na kamfanin Mikano da transfomar lantarki guda ɗaya.

Sai dai jami’an sun yi nasarar shawo kan gobarar tare da hana ta bazuwa zuwa sauran sassan ginin bankin. Hukumar ta ce har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Advertisement

A wani lamari makamancin haka, gobara ta tashi da misalin ƙarfe 6:19 na yamma a Sabuwar Gandu, Sheka Gari, Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Jami’an kashe gobara daga tashar Sharada Industrial Area sun isa wurin, inda suka tarar da gobarar ta kama ɗakuna biyu, falo da ɗakin girki na wani gidan zama.

Hukumar ta ce an yi nasarar kashe gobarar ta hanyar amfani da bututun ruwa guda ɗaya daga motar kashe gobara ta Commando 3 ta Sharada, tare da ƙarin bututun ruwa guda biyu daga masana’antun da ke makwabtaka da wurin.

Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar a gidan.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending