News
Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutane 237 A Nijeriya Cikin Watanni Bakwai – NCDC
Aƙalla mutane 237 ne suka mutu sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a Nijeriya cikin watanni bakwai na shekarar 2026, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC).
Rahoton Yanayin Zazzabin Lassa na NCDC ya nuna cewa zuwa mako na 30 na shekarar 2026, an tabbatar da mutane 1,000 sun kamu da cutar a jihohi 23 da ƙananan hukumomi 116 na ƙasar.
Alƙaluman sun nuna cewa adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya ƙaru da kashi 23.7 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci na shekarar 2025.
A cikin makon da aka tattara bayanan, an samu mutane 227 da ake zargin sun kamu da zazzabin Lassa, inda aka tabbatar da mutane 17, yayin da mutum shida suka rasa rayukansu a jihohin Ondo, Bauchi da Benue.
Adadin sabbin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya ragu daga mutum 20 da aka samu a mako na 29. Sai dai NCDC ta ce yawan waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar da kuma waɗanda aka tabbatar sun kamu ya zarce adadin da aka samu a makamancin wannan lokaci a shekarar 2025.
Rahoton ya bayyana cewa kashi 86 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar sun kamu da zazzabin Lassa a shekarar 2026 sun fito ne daga jihohi biyar, waɗanda suka haɗa da Ondo, Bauchi, Taraba, Edo da Benue.
Jihar Ondo ce ke kan gaba da kashi 32 cikin 100 na jimillar waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, sai Bauchi da kashi 25 cikin 100. Taraba na da kashi 13 cikin 100, Edo kashi 10 cikin 100, yayin da Benue ke da kashi shida cikin 100. Sauran kashi 14 cikin 100 sun fito ne daga wasu jihohi 18.
NCDC ta ce cutar ta fi shafar mutane masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30, duk da cewa an samu rahoton kamuwa daga mutum mai shekara ɗaya zuwa mai shekara 93. Matsakaicin shekarun waɗanda suka kamu da cutar ya kai shekara 30
Haka kuma, rahoton ya nuna cewa yawan maza da mata da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kasance kusan mutum ɗaya mace ga kowane maza 0.9.
A makon da ake nazari, an kuma samu wani ma’aikacin lafiya guda ɗaya da ya kamu da zazzabin Lassa, lamarin da ya sake nuna haɗarin da ma’aikatan lafiya ke fuskanta yayin kula da masu ɗauke da cutar.
NCDC ta ce tana aiki tare da abokan hulɗarta wajen ƙarfafa sa ido kan cutar, da kuma hanyoyin rigakafi da dakile yaɗuwarta, tare da ƙara haɗin gwiwar al’umma a jihohin da cutar ta fi kamari.
Hukumar ta ƙara da cewa ta horas da ma’aikatan lafiya da ke sahun gaba, tare da ƙarfafa shirye-shiryen rigakafi, samar da kayayyakin kariya da tura ƙungiyoyin ba da agajin gaggawa na ƙasa zuwa jihohi bakwai da aka fi samun rahotannin cutar.
Bugu da ƙari, NCDC ta samar da wani shirin kariya na kwanaki 30 ga ma’aikatan lafiya, da nufin rage haɗarin yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aikatan da ke sahun gaba a jihohin da cutar ta fi kamari, tare da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka (CDC).
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
