Connect with us

News

Nada Mataimaka Na Musamman (SAs) Guda 4,000 Da Nayi Ba Matsala Ba Ce —Gwamnan jihar Edo

Published

on

Okpebholo 1783018143
Gwamnan jihar Edo sanata Monday Okpebholo

Gwamnan jihar Edo sanata Monday Okpebholo, ya ce nadin mataimaka na musamman (SAs) guda 4,000 da gwamnatinsa ta yi ba wani abu ne da ya kamata a damu da shi ba, yana mai cewa hakan na daga cikin kokarinsa na kai mulki da damar aiki zuwa matakin karkara.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar litinin yayin wani taro da ya yi da mambobin jam’iyyar APC daga kananan hukumomi 18 na jihar, a gidan gwamnati da ke birnin Benin.

Maulidi Ba Wurin Miyagun Ɗabi’u Ba Ne – Zawuyiyar Sheikh Tijjani Usman

Okpebholo ya ce nasarar da APC ta samu ba tasa kadai ba ce, illa nasarar dukkan mambobin jam’iyyar, don haka ya zama dole a tabbatar da cewa an rarraba damar gudanar da mulki zuwa ga ‘yan jam’iyyar tun daga matakin jiha har zuwa mazabu da unguwanni.

Ya ce: “Nada mataimaka na musamman 4,000 ba matsala ba ce ko kadan, domin dukkanmu mun yi aiki domin wannan nasara. Wannan nasara ba ta Okpebholo kadai ba ce.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending