Connect with us

News

Gwamna Abba Kabir Ya Amince Da Karin Albashi Ga Ma’aikatan Jami’o’in Kano Guda Biyu

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin karin albashi ga malaman jami’a da sauran ma’aikatan Jami’ar Aliko Dangote ta kimiyya da fasaha da ke Wudil, da kuma Jami’ar Northwest da ke cikin garin Kano.

Sabon tsarin albashin ya samo asali ne daga sabon tsarin biyan albashin da gwamnatin tarayya ta fara amfani da shi a jami’o’in gwamnatin tarayya.

Maulidi Ba Wurin Miyagun Ɗabi’u Ba Ne – Zawuyiyar Sheikh Tijjani Usman

Sanarwar da kakakin gwamnan jihar Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin ta ce sabon tsarin zai fara aiki daga Janairu 2026, yayin da za a fara biyan sabon albashin a Satumba 2026.

Jimillar kudin da karin albashin zai ci a kowanne wata ga jami’o’in biyu ta kai Naira miliyan 391.8, wato sama da Naira biliyan 4.7 a shekara.

A Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, karin albashin zai kasance Naira miliyan 228.2 a wata, yayin da a Jami’ar Northwest da ke Kano zai kai Naira miliyan 163.65 a wata.

Advertisement

wamnatin Kano ta kuma ware Naira biliyan 1.56 a cikin kasafin kudin kari na shekarar 2026 domin biyan albashin daga Satumba zuwa Disamba 2026.

Haka kuma, za a tanadi Naira biliyan 3.13 a kasafin kudin shekarar 2027 domin biyan bashin karin albashin da ya taso daga Janairu zuwa Agusta 2026.

A cewar gwamnatin, matakin na da nufin tabbatar da zaman lafiya tsakanin ma’aikata da gwamnati, da kuma inganta jin dadin ma’aikatan jami’o’in.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending