News
KANO: Mutum 4 Daga Cikin Mutane 16 Da Wani Gini Ya Rufta A Kansu A Dala Sun Rasa Ransu
Mutane huɗu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu suka jikkata bayan wani gini mai hawa ɗaya ya rufta kan wani gida a Unguwar Dukawar Gobirawa da ke Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano.
Arewa Radio ta ruwaito cewa mutane 16 ne ginin ya rutsa da su, ciki har da mata biyu da maza biyu waɗanda suka rasa rayukansu, yayin da sauran waɗanda lamarin ya rutsa da su suka samu raunuka.
Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutane 237 A Nijeriya Cikin Watanni Bakwai – NCDC
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne bayan ginin mai hawa ɗaya ya rufta kan gidan Malam Yusuf Rabi’u, inda ya rutsa da shi da wasu daga cikin iyalansa.
Bayan faruwar lamarin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala, Malam Suraj Ibrahim Imam, ya kai ziyarar jaje ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da ziyartar waɗanda suka jikkata domin duba halin da suke ciki.
Shugaban ya jajanta wa iyalan mamatan bisa wannan babban rashi, inda ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya, sannan Ya ba iyalan haƙurin jure wannan babban rashi.
A halin yanzu, Malam Yusuf Rabi’u, wanda gidan nasa ya gamu da wannan iftila’i, yana ci gaba da karɓar magani sakamakon raunukan da ya samu.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
