Connect with us

News

Matashi Ya Rasa Ransa Yayin Kokarin Nuna Bajinta Ga Budurwarsa

Published

on

IMG 20260604 001253 779

Wani matashi ya rasa ransa bayan ya nutse a wani tafkin wanka yayin da ake zargin yana kokarin nuna bajintarsa ga budurwarsa.

Rahotanni daga shaidu sun ce matashin ya bayyana wa budurwar cewa ya iya iyo, kafin ya shiga bangaren tafkin da ruwa ya fi zurfi.

Advertisement

Sai dai jim kadan bayan shiga ruwan, ya fara nuna alamun cewa yana cikin matsala, inda daga bisani ya nutse kafin mutanen da ke wurin su yi kokarin ceto shi.

Dakarun Soji Sun Halaka Ƴan Ta’adda Sama Da 50 A Borno

Advertisement

An ce an ciro matashin daga cikin ruwan, amma kafin a kai masa cikakken agajin gaggawa tuni ya rasu.

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jama’a suka taru a wurin bayan faruwar lamarin, yayin da alhini da firgici suka mamaye masu kallo.

Advertisement

Rahotanni sun kuma nuna cewa babu jami’in ceto na tafkin (lifeguard) a bakin aiki a lokacin da lamarin ya faru, abin da ya jawo tambayoyi kan matakan tsaro da aka tanada a wurin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu karin bayani daga hukumomin da abin ya shafa kan aukuwar lamarin ba.

Advertisement

 

PLATINUM POST NEWS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending