Uncategorized
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Barazanar Sace Sarkin Ƙauye A Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu bisa zargin yi wa Sarkin Ƙauyen Bangare da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa barazanar sace shi.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Sabon Rikici Ya Barke a APC a Gombe Kan Ware Sama da Kashi 95% na ’Yan Takarar Majalisa
A cewar sanarwar, Sarkin Ƙauyen Bangare, Malam Idris, ya shigar da ƙara a ofishin ’yan sanda na Gezawa a ranar 26 ga Oktoba, 2026, inda ya ce wani mutum da bai san ko wanene ba ya kira shi ta waya a ranar 24 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 9:33 na dare, yana yi masa barazanar sace shi.
Sanarwar ta ce bayan samun ƙorafin, jami’an ’yan sanda sun fara bincike, wanda ya kai ga kama Aliyu Naziru Garba mai shekara 20 da Bashir Alhasan, mai shekara 20.
Rundunar ta bayyana cewa waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an ’yan sanda na Gezawa bisa gaggawar ɗaukar mataki kan lamarin.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan yaƙi da aikata laifuka, tare da kira ga al’umma da su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko mutum da suke zargi domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

