Connect with us

News

KANO: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2 A Gwarzo ‎

Published

on

FB IMG 1778791893573

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai mummunan hari ƙauyen Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

‎Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, inda suka shiga ƙauyen a kan babura sama da 30 suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haddasa tashin hankali da firgici a tsakanin al’umma.

Advertisement

Ƙungiyoyi 25 Sun Kalubalanci Shigar Ƙungiyar Da Suke Zargin Adawa Da Gwamnati Cikin Shirin GAVI A Kano

‎Wata majiya daga masarautar yankin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida cewa maharan sun kutsa yankin ne ta hanyar Gidan Biris, wani gari da ke kan iyakar jihohin Kano da Katsina.

Advertisement

‎Majiyar ta ce mutum biyu ne suka rasa rayukansu yayin harin, inda aka kashe mutum ɗaya a Lakwaya, yayin da aka kashe ɗayan a Gidan Biris.

‎Ta ƙara da cewa maharan sun yi awon gaba da shanun jama’a kafin isowar jami’an tsaro, waɗanda daga bisani suka shiga artabu da su.

Advertisement

‎Sai dai majiyar ta tabbatar da cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani rahoton sace mutane, duk da cewa maharan sun yi nasarar sace shanu masu yawa.

‎An kuma ce an garzaya da gawar ɗaya daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Gwarzo domin gudanar da bincike kafin daga bisani a mayar da gawar zuwa Lakwaya domin jana’iza bayan samun kwanciyar hankali.

Advertisement

‎Ƙoƙarin jin ta bakin hukumomin tsaro dangane da harin bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

‎A makon da ya gabata ma, an kai makamancin hari a unguwar Gatarin Fulani da ke yankin dagacin Nasarawa, abin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a tare da ƙara kira ga hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY NIGERIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending