News
2027: An Bukaci Obi Da Kwankwaso Su Bayyana Matsayinsu Kan Sukar Sardauna
Wani marubuci daga Jihar Bauchi, Mohamed Hussaini, ya soki jagororin jam’iyyar NDC, wato Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, kan abin da ya kira rashin mayar da martani ga kalaman da ya ce sun ci mutuncin marigayi Sir Ahmadu Bello.
A wata makala da ya wallafa ranar 4 ga Yunin 2026, marubucin ya ce wani mutum da aka bayyana a matsayin mai goyon bayan Obi ya yi kalamai a wani shafin yanar gizo da suka soki tarihin Sardauna da rawar da ya taka wajen gina Arewacin Najeriya.
Mutane 49 Sun Mutu A Saharar Nijar Saboda Rashin Ruwan Sha
Ya ce kalaman sun rage darajar gudunmawar da marigayi Sardauna ya bayar wajen bunƙasa ilimi, tattalin arziki da siyasar Arewa, duk da irin tasirin da ya yi a tarihin yankin.
Marubucin ya yi nuni da cewa Sardauna na daga cikin jagororin da suka kafa tubalin ci gaban Arewa, inda ya ambaci gudunmawar da ya bayar wajen kafa Ahmadu Bello University da sauran cibiyoyin raya tattalin arziki da ci gaban al’umma.
A cewarsa, duk wani ɗan siyasar da ke neman goyon bayan al’ummar Arewa ya kamata ya fito fili ya yi tir da duk wani kalami da zai zubar da mutuncin manyan jagororin yankin, musamman idan irin waɗannan kalamai sun fito daga masu goyon bayansa.
Ya zargi Obi da Kwankwaso da kasa bayyana matsayinsu kan lamarin, yana mai cewa hakan na iya haifar da tambayoyi a zukatan masu zaɓe a Arewa yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Sai dai marubucin ya bayyana cewa al’ummar Arewa ne za su yanke hukunci kan yadda suke kallon irin waɗannan batutuwa da kuma tasirinsu ga siyasar ƙasa.
Wannan ra’ayi ne na marubucin, kuma ba lallai ne ya wakilci ra’ayin Jaridar Inda Ranka ba.
