News
Kada A Yi Wa Addini Hukunci Bisa Ayyukan Mabiyansa —Sheikh Ahmad Gumi
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya buƙaci jama’a da su riƙa tantance addinai bisa koyarwarsu da littattafansu, ba bisa ayyukan mabiyansu ba.
Jaridar The Sun ta rawaito cewa Gumi ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar.
Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta, wanda aka zargi wani ɗan ƙungiyar JIBWIS mai shekaru 22, Umar Ibrahim Gandi, da yi wa Kiristoci barazana a Enugu da Jos.
Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi Allah-wadai da abin da ke cikin bidiyon, yana mai cewa ya saɓa wa koyarwar ƙungiyar.
A nasa martanin, Gumi ya kare tarihin ƙungiyar na tsawon shekaru 47, yana mai cewa ba za a danganta ayyukan mutum ɗaya da ƙungiya baki ɗaya ba.
Ya ce ya kamata a gudanar da cikakken bincike kan wanda ake zargi, sannan a gurfanar da shi a gaban kotu idan an samu hujjojin aikata laifi.
Ya jaddada cewa adalci ya kamata ya dogara da hujjoji, ba son rai ko ra’ayin jama’a ba.

