News
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 13 Da Ake Zargi Da Ajalin Jami’in Sojan Ruwa Yayin Kwace Wayarsa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke mutum 13 da ake zargi da hannu a kisan wani jami’in sojan ruwa, Laftanar Commodore M. Buba, wanda wasu da ake kyautata zaton masu satar waya ne suka yi ajalinsa a unguwar Kawo da ke cikin birnin Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:20 na safiyar Lahadi, a kusa da gadar Kawo, lokacin da marigayin, wanda ɗalibi ne a Makarantar Jami’an Tsaro ta Kasa (AFCSC), da ke Jaji, ya tsaya domin gyara tayar motarsa.
Bayanai daga rundunar sun nuna cewa, yayin da marigayin ke kokarin sauka daga motarsa domin canza tayar, wani mutum da ake zargin mai laifi ne ya bayyana tare da bukatar ya mika masa wayarsa ta hannu.
Sai dai jami’in ya ki amincewa da hakan, wanda hakan ya fusata mai laifin, ya kuma ciro wata wuka ya soka masa a kirji.
An bayyana cewa bayan faruwar lamarin, mazauna yankin da suka ga abinda ya faru sun farmaki wanda ake zargin, inda suka yi masa dukan kawo wuka har ya rasa ransa a wurin.
Marigayin jami’in soja ya rasu yana kan hanyarsa zuwa Asibitin Manaal, inda aka tabbatar da mutuwarsa da isowarsa.
Biyo bayan wannan mummunan lamari, rundunar ’yan sanda ta gudanar da samame a unguwar Kawo, inda ta cafke mutum 13 da ake zargi da hannu a cikin lamarin. An kama su ne dauke da wukake da sauran muggan makamai.
DSP Mansir ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike tare da shirin gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
