News
Buratai Ya Karyata Rahoton Harin Boko Haram
Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya kuma tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd), ya karyata rahotannin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta na cewa ‘yan Boko Haram sun kai masa hari a lokacin bukukuwan Sallah.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da makusancinsa, kuma tsohon Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar SK Usman (rtd), ya fitar a ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025.
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 11 Da ‘Yan Bindiga Su Kai Ƙoƙarin Garkuwa Da Su
A cewarsa, labarin da ke yawo a dandalan sada zumunta kan wani hari da aka ce an kai wa Buratai, karya ce tsagwaronta, domin kuwa babu irin hakan da ta faru.
“Janar Buratai yana Abuja, inda ya gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali tare da iyalansa da abokansa, ba tare da wani abu makamancin hari ko barazana ba,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa yaɗa irin waɗannan jita-jita marasa tushe da makama, alama ce ta rashin kishin ƙasa, da kuma yunƙurin tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma.
“Wannan nau’in jita-jita da aka saba gani daga wasu marasa kishin kasa ne, wadanda ke ƙoƙarin bata suna da tayar da hankalin jama’a ta hanyar yaɗa ƙaryar da ba ta da wata alaka da gaskiya,” in ji SK Usman.
Ya shawarci jama’a da su rika tantance sahihancin duk wani bayani da suke samu, musamman a kafafen sada zumunta, kafin yada shi, domin kauce wa ɗora al’umma kan hanyar rudani da tashin hankali.
