News
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 11 Da ‘Yan Bindiga Su Kai Ƙoƙarin Garkuwa Da Su
Haɗin gwiwar jami’an tsaro da ke zirga zirga a garin Ɗanmusa zuwa ƙauyen Mara Ɗangeza a ƙaramar hukumar Ɗanmusa suka sami nasarar kuɓutar da waɗannan mutane da ‘yan bindigan da suka yi ƙoƙarin garkuwa da su.
A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun jami’in huɗɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanya wa hannu mutanen gaba ɗaya suka kuɓuta ba tare da ko ƙwarzane ba.
A cewar DSP Abubakar sai da jami’an tsaron su kai ɗauki ba daɗi da ‘yan bindigan kafin su sami nasarar kuɓutar da mutanen.
Mutanen da suka kuɓuta akwai mata tara da maza biyu waɗanda da a cikin su mutum tara sun fito ne daga ƙauyen Damuwa a ƙaramar hukumar ƙanƙara,biyun kuma daga ƙauyen Bakan da Maijidda Fahat a ƙananan hukumomin Musawa da Ɗanmusa.
Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Katsina CP Bello Shehu ya yabawa jami’an tsaron kan jarunta da suka nuna wajen samun nasarar kuɓutar da mutanen ba tare da samun raunuka ba.
Ya kuma jaddada ƙudirin jami’an tsaro a jihar na kawo ƙarshen ta’addanci a jihar da kuma kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.
CP Bello Shehu ya yi kira ga jama’a da su ba jami’an tsaron goyon bayan wajen bada bayanai na sirri na inda maɓoyan ɓata gari a faɗin jihar yake.
