Connect with us

News

Mutane 7 Sun Mutu A Mahakar Ma’adinai A  Filato

Published

on

IMG 20260814 104133 210

Akalla mutane bakwai ne su ka mutu bayan ruftawar wani ramin hakar ma’adinai a yankin Kassa da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Shaidun gani da ido sun ce ma’aikatan hakar ma’adinai da dama sun kuma samu raunuka a ya yin faruwar lamarin.

Mutane 7 Sun Mutu A Mahakar Ma’adinai A  Filato

Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Laraba a ya yin da wadanda abin ya shafa ke gudanar da aikin hakar ma’adinai a wurin.

Wani mazaunin yankin, Albert Danlami, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na dare.

Danlami ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin kasa biyo bayan ruftawar, lamarin da ya sa mazauna yankin da sauran ma’aikatan hakar ma’adanan su ka fara kokarin ceto mutanen.

Advertisement

Mai magana da yawun kungiyar matasan Berom Rwang Tengwong ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ma’aikatan hakar ma’adanan bakwai ne su ka rasa rayukansu, inda ya ce an yi kokarin ceto ma’aikatan bayan faruwar lamarin, sai dai an dauko wasu ba tare da rai ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending