Connect with us

News

Yara 875,593 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Kano — Gwamnati

Published

on

Out of School Children Kano (1)

Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Kano ya ragu da kashi 11.5 cikin 100, daga 989,234 a shekarar 2023 zuwa 875,593 a sabon binciken shekarar 2026.

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta bayyana cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar ya ragu da yara 113,641 cikin shekaru uku, sakamakon matakan da ake dauka wajen inganta harkar ilimi.

‎ICPC Ta Gano Wani Jami’in Da Ya Sanya Matarsa, ’Ya’yansa Da ’Yan Uwansa 14 Cikin Masu Karɓar Albashin Gwamnati

Kwamishinan Ilimi na jihar, Gwani Dr Ali Haruna Abubakar Makoda, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton binciken yaran da ba sa zuwa makaranta na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Zauren COVID-19 na Ma’aikatar Ilimi da ke Kano.

Makoda ya ce sabon binciken ya nuna cewa adadin yaran da ba sa cikin tsarin karatun boko ya ragu daga 989,234 a shekarar 2023 zuwa 875,593 a shekarar 2026, wanda ke nuna raguwar kashi 11.5 cikin 100.

Sai dai ya jaddada cewa har yanzu akwai babban kalubale, ganin cewa yara 875,593 ba sa zuwa makaranta, lamarin da ke bukatar karin kokari daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Advertisement

Alkaluman na shekarar 2026 sun samo asali ne daga cikakken bincike da aka gudanar a fadin Jihar Kano.

A cewarsa, binciken ya samar da sahihan bayanai da aka rarraba a kananan hukumomi, shekaru da jinsi, wadanda za su taimaka wajen tsara manufofi, rabon albarkatu da kuma aiwatar da shirye-shiryen ilimi da suka dace da bukatun al’umma.

Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwar Jihar Kano da UNICEF da sauran Ƙungiyoyi na ci gaba na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

 

 

STALLION TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending