Connect with us

News

Karancin Ma’aikatan Jinya Na Barazana Ga Kula Da Masu Cutar Kansa A Najeriya

Published

on

rare ovarian cancer
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Masana harkar jinya sun yi gargaɗin cewa ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan jinya da ke kula da masu fama da cutar kansa na kawo cikas ga ingancin jinya a Najeriya.

Sun buƙaci gwamnati ta inganta walwala da yanayin aikin ma’aikatan, tare da faɗaɗa damar samun horo domin ƙara yawan ƙwararru a fannin.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Huɗu Kan Zargin Satar Kayayyakin Layin Dogo A Katsina

Bayanai daga Cibiyar Bincike da Kula da Cututtukan Daji ta Ƙasa (NICRAT) sun nuna cewa Najeriya na samun sabbin masu cutar kansa tsakanin 102,000 zuwa 127,763 a kowace shekara, yayin da adadin waɗanda ke mutuwa sakamakon cutar ya kai tsakanin 72,000 zuwa 79,542.

Farfesa Khadijat Musah ta bayyana cewa ƙwararrun ma’aikatan jinya da ke kula da masu cutar kansa kusan 300 ne kawai a Najeriya.

Ta ce ƙaurar ma’aikatan lafiya zuwa ƙasashen waje domin neman ingantacciyar rayuwa da yanayin aiki na ƙara ta’azzara matsalar ƙarancin ƙwararru a ƙasar.

Advertisement

Musah ta kuma bayyana cewa cibiyoyi biyu ne kawai ke bayar da horon musamman ga ma’aikatan jinya a fannin kula da masu cutar kansa a Najeriya.

Ta jaddada buƙatar gwamnati ta inganta walwala da yanayin aikin ma’aikatan, tare da ƙara yawan cibiyoyin horo domin tabbatar da samun isassun ƙwararru.

Haka kuma, Mataimakiyar Shugabar Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya Masu Kula da Cutar Kansa ta Najeriya, Fatima Adam, ta ce ƙwararrun ma’aikatan jinya na da muhimmiyar rawa wajen kula da masu fama da cutar kansa.

A nata ɓangaren, Nanre Mampak ta yi kira ga gwamnati da ta riƙa shigar da ma’aikatan jinya cikin yanke shawarar da ta shafi harkokin lafiya, domin amfani da ƙwarewarsu wajen inganta tsarin kiwon lafiya a Najeriya.

Masana sun ce magance ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan jinya na da muhimmanci wajen inganta kula da masu cutar kansa da rage matsalolin da marasa lafiya ke fuskanta.

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending