News
EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na Shekarar 2026
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta buɗe shafin neman aiki a hukumar na shekarar 2026, inda ta gayyaci ƴan Nijeriya da suka cancanta su nemi guraben aiki a sassa daban-daban na hukumar.
Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa masu sha’awar neman aikin za su iya cike fom ɗinsu ta intanet ta shafin ɗaukar ma’aikatan hukumar.
Duk Wanda Ya Kamu Da Cutar Ebola Zai Rabauta Da N100,000 Duk Mako — Gwamnatin Tarayya
Guraben aikin sun haɗa da jami’an bincike masu manyan muƙamai, da jami’an bincike, da mataimakan jami’an bincike da kuma ƙwararrun ma’aikata a fannoni daban-daban. Waɗannan fannoni sun haɗa da shari’a, da likitanci, da jinya, da fannin magani, da injiniyanci, da fasahar sadarwa (ICT), da lissafin kuɗi, da yaɗa labarai, da gudanarwa da kula da ma’aikata.
Dangane da sharuɗɗan neman aikin, masu neman matsayin jami’in bincike mai babban matsayi dole ne su kasance da digiri ko Babbar Difloma ta Ƙasa (HND), tare da takardar kammala bautar ƙasa (NYSC) ko takardar keɓewa saboda shekaru.
Ana buƙatar masu neman matsayin Detective Inspector su kasance da takardar ND ko NCE, yayin da masu neman matsayin Detective Assistant za su buƙaci aƙalla maki biyar na credit a WAEC, NECO, GCE ko NABTEB, ciki har da Turanci da Lissafi.
Hukumar ta kuma buƙaci masu neman aiki su kasance ƴan Nijeriya, kuma su kasance cikin ƙoshin lafiya, su iya amfani da kwamfuta, kuma su kasance ba su da tarihin aikata laifi. An kuma sanya sharuɗɗan shekaru da suka bambanta bisa ga matsayin aikin da ake nema, inda wasu guraben ke da iyakar shekaru 25, 27 ko 30, yayin da wasu guraben ƙwararru ke kaiwa shekaru 40.
Masu sha’awar neman aikin za su iya ziyartar shafin hukuma na EFCC ta adireshin https://recruitment.efcc.gov.ng domin buɗe asusu, cike fom da loda takardun da ake buƙata. Hukumar ta jaddada cewa neman aikin kyauta ne, tare da gargaɗin masu nema da su guji biyan kuɗi ga wasu mutane domin samun gurbin aiki.
Ana kuma shawartar masu nema su tabbatar da sahihancin bayanansu kafin aikawa da fom ɗin.
-
News5 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

