Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tura Dakarun Soji 600 Zuwa Indiya Domin Samun Horon Yaki A Dazuka 

Published

on

militaryarmy 1000x600
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Rundunar Sojojin Ƙasa ta Najeriya ta fara tura jami’anta 600 zuwa Indiya domin samun horo na musamman kan dabarun yaƙi a dazuka da yankunan tsaunuka, domin ƙara ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Kakakin rundunar, Kanal Appolonia Anele, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ta ce horon zai inganta ƙwarewar sojojin wajen gudanar da ayyuka a wuraren da ke da wahalar shiga.

Ƙudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Samu Amincewar Jihohi 24

Sanarwar ta ce rukuni na farko na sojoji 300 ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026, a cikin jiragen saman rundunar sojin saman Indiya guda biyu, C-17 da Airbus A321.

Ta ce Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ne ya ƙaddamar da shirin, wanda ke cikin ƙoƙarin rundunar na inganta ƙwarewar jami’anta da shirya su tunkarar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Manjo Janar UG Yusuf, wanda ke kula da tawagar tallafi da ba da shawarwari kan horar da sojojin Najeriya, ya wakilci babban hafsan sojin wajen rakiyar jami’an da suka tashi zuwa Indiya.

Advertisement

Sanarwar ta ce horon zai bai wa sojojin ƙwarewa kan dabarun yaƙi a dazuka da tsaunuka, tare da inganta iya gudanar da ayyuka a wuraren da ke da wahalar shiga.

Ta ƙara da cewa shirin na daga cikin matakan gina rundunar soji mai ƙwarewa da kuma shiri domin yaƙi da ’yan ta’adda, masu tayar da ƙayar baya da sauran masu aikata laifuka da ke fakewa a dazuka da yankunan tsaunuka.

Haka kuma, horon zai ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Indiya, tare da taimakawa wajen kare ikon ƙasar da rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya.

Rundunar ta ce ana shirye-shiryen jigilar sauran sojoji 300 zuwa Indiya domin kammala shirin tura jami’ai 600 da za su samu horon.

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending