Connect with us

News

Jihohi 21 Ne Kawai Suka Shirya Tinkarar Cutar Ebola — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Gwamnatin Najeriya ta ce ya zuwa yanzu jihohi 21 ne kawai suka shirya tinkarar cutar ebolar da aka fara samun wadda ta kamu da ita a Abuja, yayin da jihohi 15 suka kasa ɗaukar matakin da ake buƙata.

Ministan lafiyar ƙasar Farfesa Muhammad Ali Pate ya bayyana haka, lokacin da yake ci gaba da bayani ga taron majalisar tattalin arzikin ƙasa, wanda ya ƙunshi gwamnoni da mataimakin shugaban ƙasa dangane da samun cutar.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tura Dakarun Soji 600 Zuwa Indiya Domin Samun Horon Yaki A Dazuka 

Pate ya ce waɗannan jihohi 21 sun yi duk abinda ya dace na kai ɗaukin gaggawa da zaran an samu mai ɗauke da cutar a jihohin su, yayin da ake buƙatar sauran 15 da suka rage da su ƙara ƙaimi.

Ministan ya bayyana haɗin kai tsakanin bangaren masu kula da lafiyar da shugabanni, da bincike a hanyoyin shiga jihohin da gwajin likita da kuma samarda kayayyakin aiki da kuma sadarwa a matsayin manyan batutuwan da ake buƙata.

Pate ya shaidawa taron cewar gwamnatin tarayya na haɗa kai da jihohi wajen ganin sun yi aiki tare, yayin da Cibiyar kula da yaɗuwar cututtuka ke taimakawa jihohin wajen ganin sun yi abinda ya dace.

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending