News
BAUCHI: An Kama Matar Aure Bisa Zargin Soka Wa Mijinta Wuƙa Kan Waya
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata mata mai shekara 18, Fatima Dalha, bisa zargin soka wa mijinta mai shekara 30 wuƙa a ciki sakamakon saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan kuɗi, waya da wasu kayayyaki.
Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, a yankin Lirr Bajar da ke Ƙaramar Hukumar Dass ta jihar.
Karancin Ma’aikatan Jinya Na Barazana Ga Kula Da Masu Cutar Kansa A Najeriya
Ya ce jami’an ’yan sanda sun ceto matar daga hannun fusatattun jama’a, yayin da aka garzaya da mijin zuwa asibiti, inda ake ba shi kulawar likitoci.
A cewar kakakin, an ƙwato wuƙar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin, yayin da rundunar ke shirin miƙa lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi kira ga ma’aurata da su riƙa warware saɓanin da ke tsakaninsu cikin lumana, tare da guje wa duk wani mataki da zai iya jefa rayuwa cikin haɗari.
Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai kira gare su da su riƙa kai rahoton duk wani laifi ga hukumomin da abin ya shafa.
-
News5 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

