Connect with us

News

Babbar Mai Shari’a Ta Jihar Kano Ta Saki Fursunoni Bakwai Saboda Rashin Lafiya

Published

on

IMG 20260814 WA00191 (1)

Alkaliyar babbar kotun Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin sakin fursunoni bakwai bisa dalilan rashin lafiya, bayan ta duba shari’o’in mutane 82 da ke tsare suna jiran shari’a.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya, reshen Kano, Musbahu Nassarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Yara 875,593 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Kano — Gwamnati

Sanarwar ta ce an gudanar da aikin duba shari’o’in a gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse, a wani mataki na hanzarta gudanar da shari’a da kuma kare haƙƙin mutanen da ke tsare.

Sanarwar ta ce Mai Shari’a Abdu Aboki ta duba shari’o’in mutanen da wasu daga cikinsu suka shafe shekaru a tsare ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu bisa ƙa’ida ba.

A yayin aikin, alkalin ta bayar da umarnin sakin fursunoni bakwai nan take saboda matsalolin lafiya, bayan la’akari da yanayin lafiyarsu da sauran abubuwan da suka shafi ci gaba da tsare su.

Advertisement

Mai Shari’a Abdu Aboki ta jaddada muhimmancin gudanar da shari’a cikin adalci ba tare da jinkiri ba.

A nasa jawabin, Kwamandan Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano, Ahmed Lakpene, ya shawarci waɗanda aka saki da su ɗauki ’yancinsu a matsayin wata dama ta fara sabuwar rayuwa, su kasance masu bin doka tare da guje wa duk wani abu da zai iya sake kai su ga cin karo da doka.

Lakpene ya kuma yaba wa Babban Kwamandan Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa samar da yanayin da ke ba da damar kula da fursunoni cikin mutunci.

Ya ce ayyukan sakin fursunoni na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma tabbatar da cewa kowa yana samun damar yin adalci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending