News
‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Daliban JSS 3 Guda Biyu Bisa Zargin Satar Wayoyi 100
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu dalibai matasa biyu da ake zargi da yin fashi a wani shagon sayar da wayar salula da ke Kasuwar Wunti a cikin babban birnin Bauchi.
Wadanda ake zargin, daliban ne masu shekara 15 a makarantar Bakari Dukku Comprehensive Secondary School, an ce suna da hannu wajen satar wayoyin hannu guda 100, MP4 guda 75, batirin wayar salula 30, memory card guda 50, da na’urar Bluetooth.
Fubara Ya Amince Da Biyan Mafi Karancin Albashi Na N85,000 Ga Ma’aikatan Jihar.
An kama su ne bayan wani bincike da rundunar ‘Operation Restore Peace (ORP)’ ta gudanar bayan mai shagon ya sanar da ‘yan sanda abubuwan da suka bata.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Ahmed Wakil, ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Oktoba, 2024.
Wadanda ake zargin, mai suna Hamza Sadiq da Adamu Ahmadu, an ce sun amsa cewa sun samu makullin shagon ne tare da yin amfani da rashin zuwan mai shagon inda suka rika satar kayayyaki da rana.
“’Yan sanda sun kwato wayoyin hannu guda 21, na’urar MP4 5, cajar wayar hannu, da kuma mabudin karfe daga hannun wadanda ake zargin yayin da ake ci gaba da kwato sauran kayayyakin da aka sace.
