News
Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi.
Gwamnatin Jihar Kano ta kulle wata cibiyar harkokin fina-finai da ke Unguwa Bello a yankin Dorayi, bisa zargin karya dokokin tsara gine-gine da kuma gudanar da aiki a yankin da aka ware domin gidajen zama.
An aiwatar da matakin ne a ranar Laraba a ƙarƙashin shirin “Operation Show Your Document”, wanda Kwamitin Yaƙi da Gine-ginen da Ba Su da Izini ke gudanarwa ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktan Hukumar Kula da Taswirar Filaye da Kasa (KANGIS) na jihar Kano, Dakta Dalhatu Sani Aliyu
KANO: Kwamitin Binciken KNUPDA Ya Buɗe Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe Da Shawarwarin Jama’a
Da yake jawabi yayin aikin, Dakta Dalhatu ya ce matakin ya biyo bayan korafe-korafen da mazauna yankin da wasu malamai suka shigar kan yadda ake gudanar da cibiyar a cikin unguwar.
Ya bayyana cewa binciken farko da kwamitin ya gudanar ya nuna cewa cibiyar ba ta cika wasu muhimman sharuddan doka da suka wajaba ba.
“Mun samu korafe-korafe daga al’umma da kuma wasu malamai kan wannan cibiya. Bayan binciken da muka fara gudanarwa, mun gano akwai matsaloli da dama, kuma har yanzu ba a gabatar mana da takardun da suka dace ba,” in ji shi.
Shugaban KANGIS ya kara da cewa ko da masu cibiyar suka gabatar da wasu takardu a gaba, har yanzu za a ci gaba da kallon ginin a matsayin wanda ya saɓa wa dokokin tsara birane saboda wurin da aka kafa shi.
“Ana magana ne kan yanki da kusan kashi 99 cikin 100 na gidajen zama ne. Saboda haka kafa cibiyar harkokin fina-finai a irin wannan muhalli ya saɓa wa dokokin amfani da ƙasa da tsarin gine-gine,” ya bayyana.
Dakta Dalhatu ya ce gwamnatin jihar na kuma la’akari da tasirin irin waɗannan ayyuka ga zamantakewar al’umma, musamman matasa, domin tabbatar da kyawawan ɗabi’u da ingantacciyar tarbiyya a tsakanin al’umma.
Ya yi gargaɗin cewa gwamnati ba za ta yi sassauci ga duk wani mutum ko ƙungiya da ke gudanar da ayyuka ba tare da bin tanade-tanaden doka ba.
“Duk wanda yake tunanin ya fi ƙarfin doka, to doka za ta yi aiki a kansa cikin adalci da sahihiyar hanya,” in ji shi.
Sannan ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da sauraron korafe-korafensu tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare muradunsu.
A cewarsa, wannan mataki na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da bin dokokin tsara birane tare da magance gine-gine da ayyukan da ake gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na Kano.
