Connect with us

News

Ibrahim Ali Amin Little Ya Zaɓi Abdulkadir Shehu Bari A Matsayin Abokin Takararsa A 2027

Published

on

FB IMG 1786293088101

Ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya bayyana Abdulkadir Shehu Bari a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimakin gwamna a zaɓen shekarar 2027.

Little ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce ya zaɓi Abdulkadir Shehu Bari ne bisa la’akari da ƙwarewarsa, fahimtar al’amuran al’umma da kuma irin gudunmawar da yake sa ran zai bayar wajen tafiyar da harkokin jihar.

Ibrahim Ali Amin Little Ya Ayyana Abdulkadir Shehu Bari A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027

Ya ce Abdulkadir Shehu Bari matashi ne mai ƙwarewa a fannoni daban-daban, wanda kuma yake da fahimtar ƙalubalen da al’ummar Jihar Kano ke fuskanta, tare da kishin ganin jihar ta samu ci gaba mai ɗorewa.

A cewar Little, zaɓin Bari ya kuma yi la’akari da buƙatar bai wa matasa dama su taka muhimmiyar rawa a harkokin jagoranci da gudanar da mulki.

“Abdulkadir Shehu Bari matashi ne mai ƙwarewa da hangen nesa, kuma muna ganin zai kasance muhimmin ginshiƙi wajen tabbatar da manufofinmu idan Allah Ya ba mu nasara,” in ji shi.

Advertisement

Abdulkadir Shehu Bari ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Rogo ne da ke Jihar Kano, kuma ana sa ran haɗin gwiwar ’yan takarar biyu zai ƙara wa jam’iyyar ADC ƙarfi yayin da take shirin tunkarar zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Sanarwar zaɓin Bari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa da masu neman takara ke ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Ibrahim Ali Amin Little na daga cikin ’yan siyasar da suka bayyana aniyarsu ta neman kujerar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, yayin da zaɓin abokin takararsa ke ƙara fayyace yadda tawagar za ta kasance wajen fafutukar neman mulkin jihar a 2027.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending