Connect with us

News

Kwamitin Kartakwana A Kan Katin Zaɓe Ya Nemi Limaman Juma’a Su Wayar Da Kan Jama’a A Kano

Published

on

IMG 20260625 WA0009

‎Kwamitin Kartakwana a kan Katin Zaɓe (CVR) a Jihar Kano ya buƙaci limaman masallatan Juma’a da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zaɓe da kuma shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya.

‎Wannan kira ya fito ne yayin wata ganawa da kwamitin ya yi da limaman masallatan Juma’a, inda Shugaban Ƙaramin Kwamitin Hulɗa da Malamai, Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa, ya jaddada muhimmancin rawar da malamai ke takawa wajen isar da saƙonnin da suka shafi ci gaban al’umma.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi. ‎

‎Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana cewa malamai na da tasiri mai girma a cikin al’umma, don haka haɗin gwiwarsu zai taimaka wajen ƙarfafa jama’a su fito su yi rajista tare da sabunta katin zaɓensu kafin wa’adin da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) ta gindaya.

Advertisement

‎A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin na Jiha kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda Comrade Abbas Ibrahim ya wakilta, ya ce limaman Juma’a na daga cikin manyan ginshiƙan wayar da kan jama’a kan batutuwan da suka shafi ci gaban al’umma da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Advertisement

‎Ya ce kwamitin ya yi amanna cewa saƙonnin da limamai ke isarwa daga mimbari za su taimaka wajen ƙara yawan masu rajistar zaɓe, musamman matasa da mata, domin tabbatar da cewa kowa ya samu damar amfani da haƙƙinsa na zaɓe.

Advertisement

‎Wakilin shugaban kwamitin ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su rungumi shirin sabunta rajistar zaɓe tare da tabbatar da cewa sun mallaki katin zaɓensu, yana mai cewa katin zaɓe wata muhimmiyar hanya ce ta zaɓar shugabanni nagari da kuma tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyya.

Advertisement

‎Ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kai a sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da cewa saƙon muhimmancin katin zaɓe ya isa ga kowane ɗan ƙasa da ya cancanci yin zaɓe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending