Connect with us

News

Farashin Fetur Ya Ki Sauka A Najeriya Duk Da Faduwar Farashin Ɗanyen Mai A Kasuwannin Duniya

Published

on

petr
Advertisements
ads

Duk da saukar da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya bayan kwanciyar hankali da aka samu a rikicin Gabas ta Tsakiya, har yanzu farashin fetur bai sauka yadda ake zato ba a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya ragu sosai bayan tashin da ya yi sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, wanda ya haddasa fargabar tangarɗa ga harkokin samar da mai a duniya.

Rikicin ya kuma haifar da damuwa kan yiwuwar rufe mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanyar safarar mai da kusan kashi 20 cikin 100 na man da ake amfani da shi a duniya ke bi ta cikinta.

Sai dai bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikicin, farashin ɗanyen mai ya fara komawa matakan da yake a kai kafin tashin hankalin.

Ko da yake farashin mai ya ci gaba da raguwa a kasuwannin duniya, raguwar da aka samu a farashin fetur a Najeriya ba ta wuce naira 75 ba a wasu wurare.

Ya zuwa ranar Laraba, farashin ɗanyen mai ya koma kusan matakin da yake a kai kafin ɓarkewar rikicin, amma hakan bai haifar da sauyi mai yawa ga masu amfani da fetur a Najeriya ba.

Advertisement

Wasu daga cikin ‘yan ƙasar da suka zanta da manema labarai sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda har yanzu suke sayen litar fetur sama da naira 1,000, musamman a jihohin Arewacin Najeriya.

Masana harkokin tattalin arziki na danganta jinkirin saukar farashin fetur da wasu abubuwa da suka haɗa da canjin kuɗaɗen waje, tsadar sufuri da kuma tsarin kasuwancin man fetur da ake gudanarwa a ƙasar.

 

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending