Connect with us

Uncategorized

Sarkin Daura Ya Bukaci Sabon Sarkin Takutahar Ƙasar Hausa, Sheikh Abdulkadir Jiyali, Ya Yi Duk Mai Yiwuwa Domin Ci Gaban Najeriya

Published

on

IMG 20260807 214824 917

Muna kira ga Sabon Sarkin Takutahar Kasar Hausa Sheikh Jiyali Abdulkadir yayi dukkan abunda ya kamata domin kawowa Najeriya cigaba – Sarkin Daura.

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji (Dr.) Umar Farouk Umar, ya yi kira ga sabon Sarkin Takutahar Ƙasar Hausa, Sheikh Abdulkadir Jiyali, da ya yi amfani da matsayin da aka ba shi wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Sarkin Daura ya bayyana hakan ne a lokacin bikin naɗa Sheikh Abdulkadir Jiyali a matsayin Sarkin Takutahar Ƙasar Hausa na farko a tarihin masarautun ƙasar Hausa da ke Najeriya.

“Idan Aka Yi Maguɗi A Zaɓen Gwamnan Jihar Osun, Zan Kai Ƙorafi Wajen Trump” – Davido

A cewar Sarkin Daura, an zaɓi Sheikh Jiyali ne saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen hidimtawa al’umma da kuma ƙoƙarinsa na cusa wa matasa ƙaunar Annabi Muhammadu (SAW), tare da inganta tarbiyya da ɗabi’u nagari.

Ya kuma buƙaci sabon Sarkin Takutahar da ya ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan da za su ƙarfafa zaman lafiya, kwanciyar hankali da haɗin kan al’umma, musamman tsakanin matasa.

Advertisement

Haka kuma, Sarkin Daura ya shawarce shi da ya gudanar da wannan sabon nauyi cikin adalci, biyayya da hikima, tare da ci gaba da haɗa kan al’umma domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Da yake nasa jawabin bayan karɓar sarautar, Sheikh Abdulkadir Jiyali ya bayyana godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Daura bisa wannan karramawa da aka yi masa.

Ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin jajircewa da gaskiya, tare da ƙara inganta harkokin Takutaha da kuma ci gaba da hidimtawa addini da al’umma kamar yadda aka saba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending