News
Matashiya TV Za Ta Bai Wa Ma’aikatan Rediyo Ammasco Horo A Kan Daukar Hoto Da Bidiyo
Shugaban Matashiya TV Abubakar Murtala Ibrahim ne ya sanar da haka a wata wasiƙar yabawa da godiya da ya bai wa shugaban kamfanin Ammasco Alhaji Mustapha Ado Muhammad ranar Alhamis.
Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 6/8/2026, ta yabawa shugaban kamfanin Ammasco bisa yadda ya ke ƙoƙari wajen ganin matasa sun samu cigaba a al’amuransu da kuma kulawa da ma’aikatan da ke ƙarƙashinsa.
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
Shugaban Matashiya TV ya ce shigowar kamfanin Ammasco a gasar sana’o’i da Matashiya TV ta shirya ya sake tabbatar da kishin matasan da shugaban Ammasco ke da shi wajen ganin matasa sun tsaya da ƙafarsu.
Ya ce ra’ayi da kishin matasa ya zo a daidai lokacin da matasan ke buƙatar kulawa ta musamman tare da bijiro da hanyoyin da za su ƙarfafa musu gwiwa don ganin an kawar da tunaninsu daga aikata laifuka.
A sakamakon haka Matashiya TV ta bayar da dama domin horas da ma’aikatan gidan rediyon yadda za su samu ƙwarewa a ɗaukar hoto da bidiyo kuma kyauta.
Wannan dai na a matsayin tukwici da a ka ce yabawar kyauta ne.
Shugaban Ammasco Alhaji Mustapha Ado Muhammad ya ce za su ci gada da bayar da gudunmawa a harkokin matasa ta kowacce fuska kuma a kowanne lokaci.
Za a bayar da horon ne a watan Satumba mai kamawa.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
