News
Jami’an NSCDC Sun Bankado Wani Wurin Hada Gurbataccen Lemun Kwalba A Legas
Jami’an Hukumar Sibil Difens NSCDC sun kama wasu mata biyu da ake zargi da haɗa gurɓataccen lemun kwalba a yankin Badagry na Jihar Legas.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta fitar ranar Talata, inda Kwamandan NSCDC na Jihar Legas, Adedotun Keshinro, ya ce jami’an hukumar sun kai samame wurin ne a ranar 19 ga Satumba.
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
Ya ce jami’an sun fuskanci turjiya daga wasu matasa a yankin yayin gudanar da samamen, amma daga bisani suka samu nasarar bankado wurin da ake gudanar da aikin.
A cewar kwamandan, an gano wurin a kan titin Talabi Onilegbale da ke Aradagun, Badagry, inda ake zargin ana haɗa wani nau’in lemun kwalba mai suna Barkas Juice.
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun kama mata biyu da ake zargi da hannu wajen gudanar da aikin, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
