Connect with us

News

‎SERAP Da NGE Sun Bukaci Gwamnatin Tinubu Ta Daina Amfani Da Dokar Laifukan Yanar Gizo

Published

on

Kungiyar Kare Hakkokin Jama’a da Tabbatar da Daidaito (SERAP) tare da Kungiyar Editocin Najeriya (NGE), sun bukaci Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta daina amfani da dokar laifukan yanar gizo wajen murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki, musamman ga ‘yan jarida.

‎A cewar kungiyoyin, ana amfani da dokar ne domin cin zarafin mutane da ke bayyana ra’ayoyinsu cikin lumana, abin da suka ce yana nuna cewa gwamnati ba ta da niyyar mutunta hakkokin dan Adam.

Advertisement

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Bama-bamai 942 A  Zamfara

‎Sun ce wannan doka tana ci gaba da yin tasiri wajen tsare mutane bisa dalilan da suka saba wa tsarin mulki da kuma ka’idojin kare hakkin bil’adama na duniya.

‎“Amfani da irin wadannan dokoki da ba su da daidaito yana ruguza dimokuradiyya da tafiyar da mulki bisa doka a kasar nan,” in ji wata sanarwa da suka fitar.

Advertisement

‎SERAP da NGE sun kuma bukaci a gaggauta sako dukkan wadanda ake tsare da su a fadin kasar nan bisa amfani da dokar laifukan yanar gizo, wadda suka bayyana a matsayin doka da ke hana ci gaban kafafen yada labarai.

‎A shekarar 2022, Kotun ECOWAS ta bayyana wani sashi na tsohuwar dokar laifukan yanar gizo a matsayin mai danniya, tare da umartar Najeriya da ta soke shi.

Advertisement

‎Ko da yake an yi gyara a shekarar 2024, kungiyoyin sun ce har yanzu ana amfani da dokar ta hanyar da ke tauye ‘yancin jama’a.

‎Sun ce sun shigar da kara a gaban Kotun ECOWAS domin kalubalantar sabuwar dokar, suna neman a ayyana ta a matsayin sabawa kundin tsarin mulki da dokokin kasa da kasa.

Advertisement

‎Har yanzu ba a sanya ranar sauraron karar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending