Connect with us

News

2027: Ana Zargin Wike Da Gwamnonin PDP Sun Cimma Yarjejeniya

Published

on

Wike Ya Dakatar Da Sakatare Janar Na Hukumar FCDA Har Sai Baba Ta Gani

Gabanin zaɓen 2027, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP sun amince da wani matakin sulhu domin farfaɗo da jam’iyyar daga rikicin da ke addabarta.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar The Punch cewa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ne ya wakilci takwarorinsa a wata ganawa da Wike a birnin Legas. Ganawar ta mayar da hankali kan rikicin siyasa da ya kunno kai tsakanin Wike da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, da kuma rikicin shugabanci da ke ci gaba da addabar PDP a yankin Kudu maso Kudu.

Advertisement

‎SERAP Da NGE Sun Bukaci Gwamnatin Tinubu Ta Daina Amfani Da Dokar Laifukan Yanar Gizo

Bayan ƙarewar babban zaɓen shekarar 2023, jam’iyyar PDP ta shiga cikin rikice-rikicen cikin gida, lamarin da ya kara tabarbarewa sakamakon sabanin da ya shiga tsakanin Wike da Fubara. Yunƙurin sulhu da wasu shugabannin jam’iyyar suka yi bai haifar da da mai ido ba, maimakon haka ya ƙara rura wutar rabuwar kai a cikin jam’iyyar, musamman a matakin jihohi da yankuna.

 

Advertisement

A sakamakon haka, wasu fitattun ‘yan jam’iyyar sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC. Cikin su har da Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon Gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa.

 

Advertisement

A lokacin ganawar, Wike ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyya, musamman rikicin jihar Ribas da kuma batun sakataren jam’iyyar na kasa. A nasa bangaren, Gwamna Makinde ya nuna damuwa kan yadda wasu manyan ‘yan PDP ke nuna rashin girmamawa ga gwamnonin jam’iyyar, yana mai cewa hakan yana haifar da cikas ga zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar.

 

Advertisement

Daga ƙarshe, duka ɓangarorin sun amince da janye shari’o’in da ke gaban kotu, tare da komawa teburin sulhu domin ceto jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending