Connect with us

News

FCTA Ta Ƙwace Filin Sakatariyar PDP Da Wasu Filaye 4,793 A Abuja

Published

on

FCT revocation briefing 750x430

Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCTA) ta ce za ta karɓe filaye 4,794 a Abuja daga ranar Litinin mai zuwa, saboda masu su sun gaza biyan kuɗin haya na tsawon shekaru.

Daga cikin filayen da za a kwace har da filin Sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke birnin, wanda FCTA ta riga ta kwace tun watan Maris saboda rashin biyan haya da ya ɗauki dogon lokaci.

Advertisement

Wasu Yara  3 Sun Mutu Sanadiyyar Ci Abinci Mai Guba A Katsina

Mai taimaka wa Ministan Abuja kan yaɗa labarai, Lere Olayinka ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a, inda ya ce an ɗauki matakin ne bisa doka.

 

Advertisement

Ya ce filayen da abin ya shafa na cikin manyan unguwanni kamar Central Area, Garki (1 da 2), Wuse (1 da 2), Asokoro, Maitama da Guzape.

“Ba za mu yi la’akari da ko wa ne mai filin ba, doka ce za ta yi aikinta,” in ji shi.

Advertisement

Daraktan kula da ci gaban birni a FCTA, Mukhtar Galadima ya ce daga Litinin za a kulle wuraren da abin ya shafa, tare da saka alamar hana shiga.

Ya ce FCTA za ta yanke hukunci kan yadda za a yi da filayen cikin tsarin doka.

Advertisement

A game da wadanda suka kai ƙara kotu, Galadima ya ce ba wata doka da ta hana kwace filayen, domin matakin da hukumar ta ɗauka na bisa tsarin da aka tanada.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending