News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Bankado Zambar Yanar Gizo Ta Naira Biliyan 7.7, Sun Cafke Mutane Shida A Kano, Katsina Da Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce ta bankado wata babbar zambar yanar gizo da ta janyo asarar naira biliyan 7.7.
An yi zambar ne ta hanyar karkatar da katin waya da bayanan yanar gizo na wani kamfanin sadarwa kamar yanda Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa, CSP Benjamin Hundeyin ya fitar, a ranar 28 ga Janairu, 2026, a Abuja.
Ya ce Cibiyar Yaki da Laifukan Yanar Gizo ta Kasa (NPF–NCCC) ta bayyana cewa binciken ya biyo bayan koken kamfanin sadarwa da ya lura da wasu abubuwan da ba su dace ba a tsarin cajin kudi.
Binciken ya nuna cewa wasu ma’aikatan kamfanin sun rasa tsaron bayanansu, wanda ya bai wa masu laifin damar kutsa kai cikin tsarin kamfanin.
Bayan shafe makonni ana tattara bayanai, rundunar ta kai samame a Kano da Katsina a watan Oktoba 2025. Daga bisani, an sake cafke wani mutum a Abuja.
An cafke mutane shida da ake zargi da hannu a cikin zambar: Ahmad Bala, Karibu Mohammed Shehu, Umar Habib, Obinna Ananaba, Ibrahim Shehu, da Masa’ud Sa’ad.
An kwato kayayyaki da dama da ake zargin an samo su ne daga kudaden laifin. Sun hada da:
Gidaje biyu a Kano,Kananan filayen kasuwanci guda biyu,Shagunan sayar da wayoyi da kwamfutoci, sama da kwamfutoci 400 da wayoyi kusan 1,000,Motar Toyota RAV4, da kuma, Makudan kudade a asusun banki.
Rundunar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.
