News
INEC Ta Ayyana Abiodun Oyebanji A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Ekiti
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.
INEC ta sanar da sakamakon ne a ranar Lahadi a cibiyar tattara sakamakon zaɓe da ke Ado-Ekiti, bayan kammala tattara sakamakon daga ƙananan hukumomi 16 na jihar.
Shin Nasarorin Waiya Ne Ke Haddasa Adawa Da Shi?
A cewar hukumar, Oyebanji ya samu ƙuri’u 319,224, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Wole Oluyede, wanda ya samu ƙuri’u 40,543. Ɗan takarar jam’iyyar ADC, Oluwadare Bejide, ya zo na uku bayan samun ƙuri’u 12,872.
Sakamakon ya nuna cewa Oyebanji ya yi nasara a dukkan ƙananan hukumomi 16 na jihar, abin da ya tabbatar da gagarumar nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen.
Jami’ar da ta jagoranci tattara sakamakon zaɓen ta ce Oyebanji ya cika dukkan sharuddan da kundin dokokin zaɓen Najeriya ya tanada domin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Alƙaluman Zaɓen
INEC ta bayyana cewa an kaɗa jimillar ƙuri’u 382,109, yayin da aka soke ƙuri’u 6,332 saboda kura-kurai da suka sa ba su cancanci ƙididdigewa ba.
Har ila yau, adadin masu tantance katin zaɓe ya kai 384,940, daga cikin masu rajistar zaɓe 988,251 da ke jihar.
Sauran jam’iyyun da suka fafata a zaɓen sun samu ƙuri’u kamar haka:
ADC – 12,872
ADP – 1,269
A – 564
LP – 276
SDP – 179
PRP – 163
AAC – 195
AA – 126
YPP – 98
APP – 61
APM – 59
ZLP – 113
NNPP – 35
Sake zaɓen Oyebanji ya ƙara tabbatar da rinjayen jam’iyyar APC a jihar Ekiti, inda zai ci gaba da mulkin jihar na wa’adi na biyu.
Masu nazarin harkokin siyasa sun danganta nasarar gwamnan da ayyukan gwamnatinsa a fannoni daban-daban, da kuma goyon bayan da ya samu daga manyan masu ruwa da tsaki na siyasa da na gargajiya a faɗin jihar.
Nasarar ta kuma zo ne a daidai lokacin da APC ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinta a jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya, yayin da jam’iyyun adawa suka kasa haɗa kai domin fuskantar jam’iyyar mai mulki.
