News
Shin Nasarorin Waiya Ne Ke Haddasa Adawa Da Shi?
Daga Shariff Aminu Ahlan
A siyasa, samun karɓuwa da nuna ƙwarewa a aiki kan jawo yabo daga masu goyon baya, amma a lokaci guda kan haifar da adawa daga masu ra’ayi daban-daban.
Sai dai a wasu lokuta, suka kan wuce matakin gyara kura-kurai su koma abin da wasu ke kallon yunƙurin rage tasirin mutum ko bata masa suna.
A baya-bayan nan, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kasance cikin jami’an gwamnatin da ake yawan tattaunawa a kansu a kafafen yaɗa labarai da dandalan siyasa.
Masu lura da al’amuran siyasar Kano na ci gaba da tambayar dalilin da ya sa kwamishinan ya zama cibiyar ce-ce-ku-ce daga wasu ɓangarori, duk da irin rawar da yake takawa a gwamnatin jihar.
Tun bayan hawansa mulki, Waiya ya jagoranci shirye-shirye daban-daban da suka shafi hulɗa da kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki. Daya daga cikin abubuwan da magoya bayansa ke nuna a matsayin nasara shi ne farfaɗo da ƙungiyar Gauta Club, wadda ta haɗa masu sharhi da masu gabatar da shirye-shiryen siyasa domin ƙarfafa fahimtar juna da tattaunawa cikin lumana.
Wasu na ganin cewa wannan mataki ya taimaka wajen rage zafafan kalamai da rashin da’a a wasu shirye-shiryen siyasa, tare da ƙarfafa tattaunawa mai ma’ana kan al’amuran gwamnati da siyasa.
Haka kuma, masu hulɗa da kwamishinan sun bayyana shi a matsayin jami’in gwamnati mai buɗaɗɗen ƙofa, wanda ke karɓar baƙi da sauraron korafe-korafen jama’a ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko matsayi ba.
Sai dai duk da waɗannan bayanai, hare-haren suka da ake kai masa sun ci gaba da ƙaruwa. Wasu daga cikin masu goyon bayansa na zargin cewa akwai wasu masu neman tasiri a siyasar jihar da ke ƙoƙarin rage masa farin jini saboda tasirin da yake samu a gwamnatin Kano.
Ko da yake babu wata hujja da aka bayyana a fili da ke tabbatar da waɗannan zarge-zarge, masu sharhi kan siyasa na ganin cewa irin wannan yanayi ba sabon abu ba ne a siyasa, musamman idan wani jami’i ya samu karɓuwa ko amincewa daga shugabanni da jama’a.
A gefe guda kuma, amincewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da nunawa kwamishinan ta hanyar ba shi muhimman ayyuka da wakilcin gwamnati a lokuta daban-daban na daga cikin dalilan da ke sa magoya bayansa ke ganin har yanzu yana da muhimmiyar rawa a gwamnatin jihar.
Masu nazarin harkokin siyasa sun ce a tsarin dimokuraɗiyya, suka ga jami’an gwamnati abu ne mai amfani idan an gina su kan hujjoji da manufar inganta aiki. Sai dai suna gargadin cewa ya kamata a bambanta tsakanin suka mai amfani da kuma yaƙin neman bata suna saboda muradun siyasa.
Yayin da ce-ce-ku-cen ke ci gaba da ɗaukar hankali a Kano, abin da ya rage shi ne yadda jama’a za su tantance bayanan da ke fitowa daga bangarori daban-daban, tare da duba aikin da jami’an gwamnati ke yi a zahiri.
A ƙarshe, masu lura da al’amura na ganin cewa tarihin aikin kowane jami’i da irin gudunmawar da ya bayar ga al’umma su ne abubuwan da ke tabbatar da matsayinsa fiye da ce-ce-ku-cen siyasa da ke yawo a kafafen yaɗa labarai.
Shariff Aminu Ahlan
APC Intellectual Warrior.
