News
EFCC Ta Dakatar Da Asusun Gwamnatin Osun Ne Kan Zargin Almundahanar Miliyoyin Naira
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta ce ta dakatar da asusun gwamnatin jihar Osun bisa zargin yadda aka tafiyar da wasu kuɗaɗen tallafi da na ayyukan muhalli da suka kai naira biliyan 11.
Advertisements
Advertisements
Hukumar ta ce ta fara binciken gwamnatin jihar tun watan Maris, inda ta ce wasu manyan jami’ai ciki har da babban akanta na jihar sun gurfana a gabanta.
Advertisements
WASSCE 2026: Kashi 61.5 Cikin 100 Na Ɗalibai Sun Samu Darussa Biyar Har Da Turanci Da Lissafi
Advertisements
Advertisements
EFCC ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan ta gano wasu manyan kuɗaɗe na fita daga asusun zuwa wasu kamfanoni.
Sai dai gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ce ba za su amince da abin da ya kira take haƙƙin jiha ba, yana mai cewa zai ƙalubalanci matakin a kotu.
Advertisements
