Connect with us

News

Al’ummar Lata Nna Sun Rubuta Wa Shugaba Tinubu Wasika Kan Tabarbarewar Tsaro A Kwara

Published

on

Al’ummar yankin Lata Nna da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara sun rubuta wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, buɗaɗɗiyar wasika, inda suka nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta ɗaukar matakin kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane, hare-haren ‘yan bindiga da kashe-kashen da suka ce sun addabi yankinsu.

A cikin wasikar, al’ummar sun roƙi Shugaba Tinubu da ya bayar da umarnin ƙaddamar da wani gagarumin samame na jami’an tsaro domin fatattakar ‘yan bindigar da suka kafa maboya a dazukan da ke kewaye da yankin.

Jami’an Ƴansanda Sun Ceto Yara Tara, Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Safarar Yara A Neja

Haka kuma sun buƙaci gwamnati ta tallafa wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da tabbatar musu da adalci, musamman iyalan marigayi Alhassan Ndaba da wasu mazauna biyu da aka kashe a ranar 26 ga Yunin 2026.

A cewar al’ummar, sun zaɓi gwamnati ne da fatan samun ingantaccen tsaro da kariyar rayuka da dukiyoyinsu.

“Mai Girma Shugaban Ƙasa, kada ku bari a shafe garin Lata Nna daga taswira. Ku ji kukarmu, ku kawo mana agajin gaggawa,” in ji wani ɓangare na wasikar.

Advertisement

Sun bayyana cewa kusan shekaru biyu ke nan suna fuskantar hare-haren ‘yan bindiga ba tare da ɗaukar matakin da ya dace daga mahukunta ba.

A cewarsu, mazauna yankin sun sha fama da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa, fashi da makami, mamaye gonaki da kuma cin zarafin al’umma.

Al’ummar sun ce a watan Agustan 2025, mafarauta 65 sun rasa rayukansu yayin da suka yi artabu da ‘yan bindiga a daji, inda suka ce ƙarancin makaman da mafarautan ke amfani da su ya sa suka kasa tunkarar ‘yan bindigar da ke ɗauke da manyan makamai irin su AK-47. Sun ce gawarwaki 40 ne kawai aka samu aka binne.

Sun kuma zargi cewa a ranar 15 ga Afrilun 2026 an kashe Alhassan Ndaba yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gona domin neman abin da zai ciyar da iyalansa.

Kazalika, sun ce a ranar 10 ga Yulin 2026, ‘yan bindiga sun kutsa cikin garin Lata Nna da rana tsaka, inda suka shiga gidaje suna kwashe kuɗi, kayan abinci da wayoyin hannu, sannan suka fasa shaguna tare da sace kayayyaki da kuma babura huɗu da suka ce kuɗinsu ya kai Naira miliyan 1.6.

Sun ƙara da cewa a ranar 13 ga Yunin 2026, wasu ‘yan bindiga huɗu ɗauke da makamai sun shiga garin a kan babura biyu suna yawo cikin walwala tare da neman katunan waya, fetur da sauran kayayyaki, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Advertisement

A cewar al’ummar, ranar 26 ga Yunin 2026 ita ce mafi muni a tarihinsu, bayan da ‘yan bindiga suka tare hanya guda tilo da ke shiga da fita daga garin, wadda ake amfani da ita wajen zuwa asibiti, kasuwa da kuma samun agajin gaggawa, inda suka kashe wasu mazauna biyu da ke kan hanyarsu ta komawa gida.

Sun ce washegarin ranar, 27 ga Yunin 2026, wasu mazauna da suka je neman ganyayyaki a bayan ƙauyen sun faɗa hannun ‘yan bindiga, waɗanda suka ƙwace musu wayoyin hannu da kuɗaɗensu.

A wani sabon hari kuma, al’ummar sun ce a ranar 15 ga Yulin 2026 wasu ‘yan bindiga sun yi wa wani mai sana’ar POS fashi da makami bayan ya dawo daga banki da kuɗin gudanar da kasuwancinsa, inda suka ƙwace masa dukkan kuɗin da yake ɗauke da su.

Al’ummar sun yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya a yankin, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending