Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Ceto Yara Tara, Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Safarar Yara A Neja

Published

on

Rescued Children In Niger

Rundunar ƴan sanda a jihar Neja ta ceto yara tara da a ke zargin an yi safararsu tare da kama mutane biyu a wasu sumame da jami’anta su ka gudanar.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce jami’an ofishin ƴan sanda na Madalla sun kama wani direba mai suna Dauda Ayuba bayan sun tare motarsa a kan hanyar Madalla zuwa Suleja, inda su ka tarar da ƙananan ƴan mata shida masu shekaru tsakanin bakwai zuwa 13.

Al’ummar Lata Nna Sun Rubuta Wa Shugaba Tinubu Wasika Kan Tabarbarewar Tsaro A Kwara

Bincike ya nuna cewa Ayuba ya karɓi Naira 194,000 domin jigilar yaran daga Edo zuwa Neja, inda ya yi ikirarin zai kai su makaranta, alhali a na shirin amfani da su a matsayin ma’aikatan gida, masu talla da sauran ayyukan yara domin samun kuɗi. An kuma ce zai riƙa karɓar Naira 10,000 a matsayin lada kan kowane yaro a duk wata.

A wani samame dabam, jami’an ƴan sanda na Kpakungu sun kama wata mata mai suna Mary Anthony mai shekaru 37 tare da ƙananan ƴan mata uku masu shekaru tsakanin takwas zuwa 10 a Minna.

Ko da yake matar ta yi iƙirarin cewa iyayensu ne su ka ba ta yaran domin kai su gidan marayu, binciken ƴan sanda ya gano ba haka ba ne.

Advertisement

An miƙa dukkan waɗanda a ke zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike, yayin da a ka tuntubi iyayen yaran da a ka ceto. Rundunar ta ce ta na ci gaba da farautar sauran mutanen da a ke zargin su na cikin wannan ƙungiyar safarar yara domin gurfanar da su a gaban shari’a.

 

 

 

CHANNELSTV

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending