Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Dakile Shigo Da Kwayoyin Tramadol Miliyan 1.6 Zuwa Kano

Published

on

WhatsApp Image 2026 07 19 at 15.05.26

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ce ta kama sama da kwayoyin Tramadol miliyan 1.6 da ake shirin kaiwa jihar Kano, tare da tarwatsa wata ƙungiyar da ake zargin tana safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen Togo, Jamhuriyar Benin da Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon binciken sirri da jami’an hukumar suka gudanar kan ayyukan ƙungiyar.

Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC

A cewarsa, a ranar 2 ga watan Yuli, jami’an NDLEA sun tare wata tirela a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, inda suka gano kwayoyin Tramadol 853,000 masu ƙarfin 250mg da aka ɓoye a wani sashe da aka ƙera a ƙarƙashin motar. An kuma kama direban motar, Jabir Kabiru, mai shekaru 22.

Babafemi ya ƙara da cewa bayan kwana biyu, ranar 4 ga watan Yuli, jami’an sun sake kama wata tirela a wannan hanya, inda suka ƙwato kwayoyin Tramadol 777,000 da aka ɓoye ta irin wannan hanya. Direban motar, Muhammed Nuhu, mai shekaru 22, shi ma ya shiga hannu.

Ya ce bincike ya nuna cewa motocin biyu na da alaƙa da wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙetare iyaka, kuma dukkansu suna kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Advertisement

Hukumar ta ce wannan nasara ta biyo bayan kama wasu kwayoyin Tramadol 558,900 da aka shigo da su ta iyakar Togo da Jamhuriyar Benin a watan Yuni, abin da ya taimaka wajen gano hanyar da masu safarar ke amfani da ita.

 

 

PRNIGERIA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending