News
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
Jihar Kano ta kasance cikin jihohi 10 da suka fi tara kuɗaɗen Harajin Kayayyaki da Ayyuka (VAT) a Najeriya a farkon rabin shekarar 2026, inda ta zo a matsayi na bakwai da jimillar kuɗaɗen da suka kai biliyan ₦65.21.
Hakan na ƙunshe ne cikin sabbin bayanan da Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) ya fitar, kuma shafin TheCable Index ya wallafa, waɗanda suka nuna cewa an tara jimillar tiriliyan ₦3.78 na kuɗaɗen VAT a faɗin ƙasar tsakanin watan Janairu da Yunin 2026.
Burna Boy Da Shakira Za Su Yi Waƙa Yayin Hutun Rabin Lokaci A Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya
Rahoton ya nuna cewa Jihar Legas ce ta ci gaba da jan ragamar tara kuɗaɗen VAT, inda ta samar da tiriliyan ₦1.81, adadin da ya kai kusan kashi 47.9 cikin 100 na duk kuɗaɗen VAT da aka tara a ƙasar cikin wannan wa’adi.
Baya ga Legas, jihohin Rivers, Oyo, Babban Birnin Tarayya (FCT), Bayelsa da Delta ne suka zo a sahun gaba, yayin da Kano ta zo a matsayi na bakwai, abin da ke nuna irin muhimmancin jihar a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya.
Jerin Jihohin Da Suka Fi Tara Kuɗaɗen VAT
1. Legas – ₦1.81 tiriliyan
2. Rivers – ₦560.04 biliyan
3. Oyo – ₦253.67 biliyan
4. Babban Birnin Tarayya (FCT) – ₦182.93 biliyan
5. Bayelsa – ₦103.14 biliyan
6. Delta – ₦102.06 biliyan
7. Kano – ₦65.21 biliyan
8. Akwa Ibom – ₦52.89 biliyan
9. Edo – ₦51.91 biliyan
10. Borno – ₦38.38 biliyan
11. Adamawa – ₦36.69 biliyan
12. Ondo – ₦34.22 biliyan
13. Kwara – ₦33.58 biliyan
14. Jigawa – ₦33.23 biliyan
15. Ogun – ₦26.43 biliyan
16. Katsina – ₦25.82 biliyan
17. Gombe – ₦25.78 biliyan
18. Anambra – ₦24.55 biliyan
19. Sokoto – ₦23.96 biliyan
20. Plateau – ₦23.37 biliyan
21. Taraba – ₦22.14 biliyan
22. Kaduna – ₦21 biliyan
23. Zamfara – ₦20.74 biliyan
24. Ekiti – ₦20.44 biliyan
25. Ebonyi – ₦18.96 biliyan
26. Kogi – ₦18.15 biliyan
27. Yobe – ₦16.43 biliyan
28. Nasarawa – ₦16.35 biliyan
29. Kebbi – ₦15.55 biliyan
30. Imo – ₦14.64 biliyan
31. Niger – ₦14.32 biliyan
32. Benue – ₦14.10 biliyan
33. Bauchi – ₦13.39 biliyan
34. Osun – ₦13.25 biliyan
35. Enugu – ₦12.35 biliyan
36. Cross River – ₦10.55 biliyan
37. Abia – ₦8.77 biliyan
Masana tattalin arziki sun ce duk da matsayin da Kano ta samu, har yanzu akwai buƙatar ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci, masana’antu da zuba jari domin ƙara yawan kuɗaɗen VAT da jihar ke samarwa, la’akari da yawan al’ummarta da kuma matsayinta a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya.
