Connect with us

News

Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Mutunta Bukatar Iyalan Mary Habila Na Binne Ta Cikin Sirri

Published

on

images (15)

Sanatan Kaduna ta Kudu, Sunday Katung, ya bukaci al’umma da su mutunta bukatar iyalan marigayiya Mary Habila na gudanar da jana’izarta cikin sirri, yana mai kira ga jama’a da su guji duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga binciken da hukumomi ke yi kan rasuwarta.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Midat Joseph, ya fitar a ranar Asabar, Katung ya ce duk da alhini da jimamin da rasuwar Mary ta haifar, wajibi ne a kiyaye doka da oda tare da bai wa hukumomin da abin ya shafa damar gudanar da bincikensu cikin kwanciyar hankali.

Al’ummar Lata Nna Sun Rubuta Wa Shugaba Tinubu Wasika Kan Tabarbarewar Tsaro A Kwara

Sanatan ya ce iyalan marigayiyar sun bukaci a bar su su yi makoki cikin nutsuwa tare da binne diyarsu cikin mutunci, ba tare da sake fitar da gawarta domin gudanar da wani bincike ba.

Ya kara da cewa iyalan ba sa son a rika yada jita-jita ko zarge-zargen da ba su da tushe, yana mai cewa hakan na iya kara musu radadi tare da shafar binciken da ake yi.

Katung ya bayyana cewa rokon ya shafi takwarorinsa a Majalisar Dokoki ta Kasa da kuma daukacin masu yi wa iyalan ta’aziyya daga sassa daban-daban na Najeriya da ma kasashen waje, wadanda suka tuntube shi domin neman karin bayani kan lamarin.

Advertisement

Ya bayyana rasuwar Mary Habila a matsayin babban rashi ga iyalanta, abokanta da al’ummar Kaduna ta Kudu, tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar.

Sanatan ya kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya da adalci domin gano musabbabin rasuwar, yana mai jaddada cewa dole ne a mutunta hakki da bukatun iyalan marigayiyar yayin gudanar da binciken.

Hakazalika, ya tabbatar wa iyalan cewa ofishinsa zai ci gaba da bibiyar lamarin tare da tabbatar da cewa sun samu adalci da kuma amsoshin tambayoyin da suke nema bisa tanadin doka.

Marigayiya Mary Habila na cikin tawagar ma’aikatan lafiya da suka raka Ministan Ayyuka na Tarayya, David Umahi, zuwa garinsu na Uburu da ke karamar hukumar Ohaozara ta Jihar Ebonyi, inda daga bisani aka tsinci gawarta a harabar gidan ministan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending