News
Mutane 8 Sun Mutu, 17 Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Mota A Katsina

Akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 17 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar Funtua–Katsina, a yankin Layin Kukah da ke Ƙaramar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), reshen Jihar Katsina, ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta bayyana cewa lamarin ya auku da misalin ƙarfe 1:32 na rana a ranar Lahadi.
KOGI: Ana Zargin Dangin Ɗalibi Sun Kashe Malamar Makaranta Saboda Ta Ladabtar da Shi
Mai magana da yawun hukumar kan harkokin wayar da kan jama’a, DRC Shamsudeen Babajo, ya ce hatsarin ya rutsa da motar kasuwanci kirar Toyota Hiace mai lambar rajista 14B 92 TR da kuma babur mai ƙafa uku (Adaidaita Sahu) kirar Bajaj wanda ba shi da lambar rajista.
A cewarsa, mutane 25 ne ke cikin hatsarin, inda takwas daga cikinsu suka mutu, yayin da sauran 17 suka samu raunuka daban-daban.
Babajo ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya samo asali ne sakamakon wuce gona da iri da ɗaya daga cikin direbobin ya yi.
Ya ƙara da cewa hukumar ta samu rahoton hatsarin cikin mintuna kaɗan bayan faruwarsa, kuma tawagar ceto ta isa wurin domin gudanar da aikin ceto tare da haɗin gwiwar Community Watch Corps (C-Watch).
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Bakori Comprehensive domin samun kulawar likitoci, yayin da aka kai gawarwakin mamatan zuwa Babban Asibitin Funtua domin ci gaba da gudanar da matakan da suka dace.
