Connect with us

News

Gwamnatin Katsina Ta Tabbatar Da Rasuwar Janar Rabe Abubakar A Hannun ’Yanbindiga

Published

on

17813511969643269572540092512967

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon janar na soja mai ritaya, Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ’yanbindiga.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Nasiru Mu’azu, ya fitar a ranar Asabar, gwamnatin ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon suga da hawan jini.

Advertisement

Sanarwar ta ce duk da kokarin da gwamnatin jihar da jami’an tsaro suka yi domin ganin an kubutar da shi cikin koshin lafiya, hakan bai samu ba, lamarin da ya kai ga rasuwarsa a hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamnatin ta bayyana cewa rasuwar Janar din ba asara ce ga iyalansa da al’ummar Katsina kadai ba, har ma babban rashi ne ga daukacin Najeriya.

Advertisement

 

Da yake jajanta wa iyalan mamacin, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana lamarin a matsayin wani lokaci mai matukar bakin ciki, yana mai cewa hakan ya sake nuna bukatar hada kai da kara kaimi wajen yaki da miyagun laifukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

Advertisement

 

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin ganin an gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan ta’asa a gaban kuliya.

Advertisement

Haka kuma ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin Katsina ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar ’yanbindiga da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnatin ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljanna ta zama makomarsa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending