Connect with us

News

MAAUN ta taya Farfesa Amina Salihi Bayero murnar cika shekaru 56

Published

on

FB IMG 1781308198241

Rukunin Jami’o’in Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ya taya Mataimakiyar Shugabar Jami’ar Northwest University Kano, Farfesa Amina Salihi Bayero, murnar cika shekaru 56 da haihuwa.

Sakon taya murnar na kunshe ne cikin wata sanarwa da wanda ya kafa jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.

Advertisement

Jami’an EFCC Sun Cafke Jami’in Tsaro Kan Zargin Safarar Zinaren Naira Biliyan 4.4 A Kano

Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu ta Afirka (AAPU), ya bayyana cewa Farfesa Amina Salihi Bayero ta cancanci a yi mata wannan gagarumar murna saboda gudunmawar da take bayarwa ga harkar ilimi.

Advertisement

Ya ce: “Cikin godiya ga Allah Madaukakin Sarki, muna taya fitacciyar masaniya kuma mace ta farko da ta zama Shugabar Jami’ar Northwest University Kano, Farfesa Amina Salihi Bayero, murnar wannan rana mai albarka.

“A madadin mahukuntan rukunin jami’o’in MAAUN, ina mika sakon taya murna da fatan alheri ga Farfesa Amina Salihi Bayero bisa wannan muhimmin mataki da ta kai a rayuwarta.”

Advertisement

Farfesa Gwarzo ya bayyana mai bikin a matsayin abar koyi a fannin ilimi da kuma tawali’u, wadda ta yi aiki a mukamai daban-daban na ilimi da gudanarwa cikin kwarewa da nagarta.

Ya kuma yi mata addu’ar samun tsawon rai, lafiya da karin nasara domin ta ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ci gaban ilimi da take yi a jami’ar.

Advertisement

Har ila yau, wanda ya kafa jami’o’in MAAUN ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ci gaba da yi mata jagora tare da ba ta hikima da basirar da za su taimaka mata wajen daukaka jami’ar zuwa matsayi mafi girma da martaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending