News
Jihar Kano Ta Shirya Tsaf Domin Kafa ’Yansandan Jiha — Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jihar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin kafa rundunar ’Yansandan Jiha da zarar an samar da tanadin doka da kundin tsarin mulkin ƙasa da zai ba da damar hakan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwar Hukumomi Kan Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano.
Uba Ya Nemi Kotu Ta Tilasta Wa ’Yarsa Ta Fitar Da Mijin Aure A Kaduna
Abba Kabir Yusuf ya ce rundunar ’Yansandan Jiha ba za ta maye gurbin Rundunar ’Yansandan Najeriya ba, illa za ta yi aiki tare da ita domin ƙarfafa tsaro, inganta musayar bayanan sirri da kuma hanzarta ɗaukar matakan da suka dace wajen daƙile barazanar tsaro.
Ya bayyana cewa Jihar Kano na da isassun ƙwararrun ma’aikata, cibiyoyi da kuma ingantaccen tsarin gudanarwa da za su ba ta damar tafiyar da rundunar cikin nagarta idan aka amince da kafa ta.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga duk wani sahihin tsari da zai ƙarfafa tsaron ƙasa da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewarsa, ƙaddamar da kwamitin yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na nuna ƙudirin gwamnatin jihar na tinkarar matsalar ta hanyar haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
A ƙarshe, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci mambobin kwamitin da aka ƙaddamar da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, ƙwarewa da jajircewa domin cimma manufofin da aka kafa kwamitin a kansu.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Jihar Kano Ta Shiga Jerin Jahohi 10 Mafi Tara Kudaden Shiga Na VAT A 2026
