Connect with us

News

Rundunar Ƴansanda Sun Fi Kowace Ma’aikata Jami’an Bogi  —Hukumar ICPC

Published

on

Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Sauran Laifuka ta ICPC ta gano jami’an ƴan sandan Najeriya na bogi guda 570, kuma su ne adadi mafi yawa da ta gano daga ma’aikatun gwamnati.

Shugaban hukumar ta ICPC, Musa Adamu Aliyu, shi ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da BBC Pidgin a ranar Alhamis.

Jihar Kano Ta Shirya Tsaf Domin Kafa ’Yansandan Jiha — Gwamna Abba Kabir Yusuf

Musa ya ce binciken da su ka gudanar a cikin kundin tsarin biyan albashi na ma’aikatun gwamnatin Najeriya sun gano adadin ma’aikatan bogi guda 908, a faɗin ma’aikatu 50 da sashe-sashe da hukumominsu.

Shugaban hukumar ya ce Rundunar Ƴan Sandan Najeriya na da ma’aikatan na bogi guda 570, fiye da rabin adadin ma’aikatan bogin da ake da su a Najeriya.

Musa ya ce a binciken da su ka gudanar, sun gano cewa adadin mutane 570 ne su ke karɓar albashi ba tare da su na yin aiki ba.

Advertisement

Ya ƙara da cewa sun kuma gano ma’aikatan na bogi mutane 19 a Ma’aikatar Tsaro, yayin da Ma’aikatar Ayyuka da kuma Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Ƙetare su ke da ma’aikatan na bogi guda 80, sai kuma Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ke da mutane 80.

Shugaban ya kuma bayyana cewa binciken nasu ya gano wani mutum da ya sanya sunayen iyalinsa a tsarin biyan albashin, inda su ke karɓar albashin mutane 12 duk wata.

Hukumar ta ICPC dai ta samu damar karɓe kuɗi kimanin naira miliyan 941 da ke da alaƙa da almundahanar biyan albashin, wanda bincikenta ya gano daga cikin kundin Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya wato IPPIS.

 

 

THE GUARDIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending