Connect with us

News

ICPC Ta Gano Ma’aikatan Bogi 908 A Wasu Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 50

Published

on

ICPC HQ FASAD 1 1

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta bayyana cewa ta gano ma’aikatan bogi guda 908 a wasu ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya guda 50, a yayin binciken da take gudanarwa kan tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati.

Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN), ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan ci gaban binciken da hukumar ke yi kan zargin tafka maguɗi da almundahana a tsarin biyan albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule Ya Sauke Kwamishinoninsa Guda 6

A cewarsa, binciken ya gano cewa an saka sunayen mutanen da ba ma’aikatan gwamnati ba cikin tsarin biyan albashi, lamarin da ya haddasa asarar maƙudan kuɗaɗe ga baitul malin gwamnati.

Aliyu ya ce binciken na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen jama’a, tare da kawar da duk wani nau’in zamba a tsarin albashin ma’aikatan gwamnati.

Ya kuma tabbatar da cewa ICPC za ta ci gaba da bincike domin gano duk waɗanda ke da hannu a wannan almundahana, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Advertisement

Shugaban hukumar ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na tsaftace tsarin gudanar da ayyukan gwamnati, da kare kuɗaɗen al’umma daga almundahana da sauran ayyukan cin hanci da rashawa.

 

 

THE CABLE 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending