Connect with us

News

Ba Za A Gudanar Da Zaɓen Gwamna A Jihohi 8 Ba

Published

on

‎Ba za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Imo, Ondo, Osun, Bayelsa, Edo, Kogi, Ekiti da Anambra tare da sauran jihohin da za su gudanar da zaɓen gwamna a babban zaɓen 2027 ba, saboda jadawalin zaɓensu ya bambanta da na sauran jihohin.

‎Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, aka buɗe lokacin yaƙin neman zaɓen gwamna da na ’yan Majalisun Dokokin Jihohi, bisa jadawalin da ta fitar na zaɓen 2027.

An Buɗe Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna Da Majalisun Jihohi A Najeriya

‎Jihohi 28 ne za su gudanar da zaɓen gwamna a shekarar 2027, inda ’yan takara daga jam’iyyun siyasa za su fara gabatar da manufofinsu ga masu zaɓe tare da neman ƙuri’unsu.

‎Za a gudanar da yaƙin neman zaɓen ta hanyoyi daban-daban, ciki har da tarukan siyasa, kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin da dokar zaɓe ta amince da su.

‎Daga cikin manyan jam’iyyun siyasar da suka tsayar da ’yan takarar gwamna a jihohin da za su gudanar da zaɓen akwai APC, NDC da ADC.

Advertisement

‎Sai dai, wasu daga cikin manyan jam’iyyun siyasar har yanzu ba su kammala kafa ko ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓensu ba, duk da fara lokacin kamfen.

‎Rahotanni sun ce jam’iyyar APC na sake nazarin wasu daga cikin naɗe-naɗen da ta yi a kwamitin yaƙin neman zaɓenta, biyo bayan koke-koke da aka samu kan wasu mambobin kwamitin.

‎Haka kuma, jam’iyyun NDC, ADC da PDP ba su kammala ƙaddamar da wasu daga cikin tsare-tsaren yaƙin neman zaɓensu ba.

‎Masana harkokin siyasa sun danganta jinkirin da wasu jam’iyyun ke fuskanta da rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓukan fidda gwani, ƙarancin kuɗaɗen gudanar da kamfen da kuma tattaunawar ƙulla ƙawance gabanin babban zaɓen.

‎A cewar jadawalin INEC, an fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ’yan Majalisar Tarayya tun ranar 19 ga Agusta, 2026.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending